Akalla mutane 8 ‘yan bindiga su ka kashe, a Wani harin da su
ka kai a karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar Atiyap Sam Timbuwak ya sanar wa manema labarai haka, inda ya ce maharan sun afka masu ne da misalin karfe 9 na safiyar Larabar da ta gabata.
Ya ce maharan sun shiga karamar hukumar ne daga wani daji da ke kusa da wurin, inda su ka rika harbi ta ko ina har su ka kashe mutane 8.
Timbuwak ya ce sun kona gidaje 5, sannan wasu mutane hudu sun ji rauni, kuma jami’an tsaro sun kai dauki bayan maharan sun gama duk abin da za su yi sun arce cikin daji.
Sam Timbuwak, ya koka da rashin zuwan jami’an tsaron da wuri, ya na mai cewa hakan ya sa maharan su ka ci karen su babu babbaka a lokacin da su ka kai harin.