Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yada Labarai: Kungiyar Kare ‘Yancin ‘Yan Jarida Ta Ce An Kashe ‘Yan Jarida 95 A Shekara Ta 2018

Kungiyar Kare ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya Reporters Sans Frontieres, ta ce kasar Afghanistan ce mafi wuyar aiki da kuma muzguna wa ma’aikatan yada labarai a shekarar da ta gabata, yayin da aka kashe jimillar ‘yan jarida 95 a bara kadai.

Haka kum, Kungiyar Tarayyar ‘Yan Jaridu ta Kasa da Kasa ta ce, akalla ‘yan jarida 95 aka kashe a shekarar da ta gabata yayin  da su ke bakin aikin su, adadin da ya zarce wanda aka samu a shekara ta 2017, amma bai kai adadin da aka samu a lokacin da aka yi fama da rikicin Iraqi da Syria.

Kisan da aka yi dan jaridar Saudiya Jamal Khashoggi, na daya daga cikin abubuwan da su ka fi daukar hankula a shekarar da ta gabata, lamarin da ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin Turkiya da Saudiya, yayin da kasashen duniya su ka yi ta tofa albarkacin bakin su akan lamarin.

A kasashen Afrika, Ma’aikatan Yada Labarai sun ci karo da matsaloli da dama a shekarar bara, wadanda su ka hada da kamawa da tsarewa, wasu lokuta ma har da duka. Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai ya ce ba za a tauye ‘yancin kafafen yada labarai a karkashin mulkin sa ba, yayinda ya jinjina wa ‘yan jaridun Nijeriya a kan yadda su ke gudanar da ayyukan su.

Exit mobile version