Home Home Yabon Gwani: Buhari Ya Cancanci Yayi Kokari Wajen Murkushe Boko Haram –...

Yabon Gwani: Buhari Ya Cancanci Yayi Kokari Wajen Murkushe Boko Haram – Wike

61
0

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kokarinsa wajen yaki da Boko Haram da ’yan bindigar da suka addabi Najeriya.


Gwamnan ya yi yabon ne a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Fatakwal ranar Lahadi, jim kadan bayan jera furanni domin bikin ranar tunawa da ’yan mazan jiya ta bana.


Wike ya ce bayan barkewar Yakin Basasa, sojoji sun shafe shekara kusan 30 suna yaki wajen kwantar da tarzoma tare da tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya.


A cewarsa, tun daga lokacin, zai yi wahala a ce ga wata shekara da sojojin suka huta ba sa aikin kwantar da wata tarzoma a ciki da wajen Najeriya.


Gwamna Wike ya kuma ce sojojin na yaki da ’yan Boko Haram da sauran ’yan ta’adda a Jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, da kuma ’yan bindiga a Jihohin Kudu maso Gabas.