Home Labaru Yabawa: ‘Dan Ganduje Ya Jinjinawa Aikin Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano

Yabawa: ‘Dan Ganduje Ya Jinjinawa Aikin Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano

94
0
images 1
images 1

Abdulaziz Ganduje, wanda ‘da ne ga tsohon gwamnan jihar Kano, wato Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhiyi Rimingado domin jinjina masa a kan aikin da yake gudanarwa.

Rahotanni sun ruwaito cewar, Abdulaziz ya kai ziyarar ce domin yabawa Rimingado a kan kokarin sa tare da goyan bayan tuhumar da ake yiwa mahaifin sa Ganduje da uwargidan sa, wadda ke mahaifiya a gareshi da kuma ‘dan uwan sa.

Sahihan bayanai sun shaida cewar, bayan yabawa da tuhumar da ake yiwa iyayen na sa, ya kuma bayyana damuwa a kan yadda aka cire sunan sa ba bisa ka’ida ba a matsayin darakta daga daya daga cikin kamfanonin da ake kara bada sanin sa ba.

A korafin da ya gabatar, Abdulaziz ya bayyana cewar wani mai harkar gine gine ya tintibe shi domin taimaka masa sayen filaye a Kano tare da masa tayin dubban daloli da kuma kamisho na naira miliyan 35.

Abdulaziz ya ce ya mika kudaden da aka canja zuwa daloli ga mahaifiyar sa, amma abin takaici bayan wata 3 sai wanda ya biya kudin ya gano cewar an sayarwa wasu mutane daban filayen, saboda haka ya bukaci a mayar masa da kudaden sa.

Tuni dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Kano ta gurfanar da tsohon gwamnan da uwargidan sa Hafsat da ‘dan su Umar Abdullahi Umar da kuma wasu mutane 5 da ake tuhuma da laifuffuka guda 8 da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma karkata dukiyar jama’a.

Leave a Reply