Home Labaru Ya Zama Wajibi A Kara Farashin Wutar Lantarki A Nijeriya – Saleh...

Ya Zama Wajibi A Kara Farashin Wutar Lantarki A Nijeriya – Saleh Mamman

659
0
Saleh Mamman, Ministan Lantarki
Saleh Mamman, Ministan Lantarki

Gwamnatin tarayya ta ce ta shirya kara farashin wutar lantarki, yayinda ta ke shirin kammala wasu ayyuka a fadin Nijeriya kamar yadda ministan lantarki Injiniya Saleh Mamman ya bayyana.

Ministan ya ce, karin farashin ya zama wajibi saboda tsadar samar da wutar lantarki a Nijeriya, kuma hakan ya na shafar kamfanonin wuta a kasar nan.

A yanzu haka an ba kamfanonin raba wutar damar sanya farashin lantarki, tare da tabbatar da jama’a su na biyan kudi ne bisa ga wutar da su ka yi amfani da ita.

Saleh Mamman ya kara da cewa, a cikin kokarin da ake yi na inganta wutar lantarki a Arewacin Nijeriya, gwamnati za ta samar da Karin karfin lantarki, don haka idan aka samu ingancin wuta ya zama wajibi a kara farashin ta, saboda dole ne masu samar da wutar su samu kudin aikin su.

A karshe ministan ya bukaci ‘yan Nijeriya su kasance masu tsoron Allah ta hanyar biyan kudin wuta, ya na mai bada tabbacin cewa gwamnati na iyakar kokarin ta wajen kammala ayyukan da ke tafiye domin inganta wutar lantarki.