Wani matashi dan shekaru 17 mai suna Ade Segun a jihar Delta, ya shiga hannun ‘yan sanda bisa laifin tsara yin garkuwa da kan sa don ya karbi Naira miliyan 20 daga hannun iyayen sa da ke garin Warri a matsayin kudin fansa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar DSP Bright Edafe ya bayyana wa manema labarai haka a garin Asaba, inda ya ce rundunar ta kuma kamo abokan harkallar matashin su biyu da su ka hada da wani Precious da Nonso.
Edafe, ya ce Segun ya tsara sace kan sa ne tare da hadin bakin wasu abokan sa domin damfarar iyayen sa, inda abokan su ka kira iyayen Segun a wayar tarho, su ka bukaci a ba su Naira miliyan 20 a matsayin kudin kafin su saki Segun.
Ya ce iyayen Segun sun kai rahoton maganar ne a ofishin ‘yan sanda da ke Warri, inda aka yi amfani da wata jami’ar ‘yar sanda da ta boye asalin ta, ta nuna cewa za ta biya su kudin fansar da su ka bukata.