Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, ya kalubalanci Shugaba Muhammadu Buhari cewa ya kama, sannan ya tsare Gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele a kan kudin makamai da Sambo Dasuki ya wahala a kan su.
Sule Lamido, ya ce kwararru biyun da su ka mika biyayyar su da da’a ga Shugaban kasa, babu mamakin an umurci daya a kan fallen takardar kawai cewa ya saki kudin daga babban bankin, yayin da aka umurci dayan ya karbi kudin sannan ya rarraba su ga wasu jerin mutane.
Ya ce dukkan su a matsayin su na masu biyayya kuma wadanda shugaban kasa ya nada sai su ka bi umurnin da aka ba su a wasikar, amma dayan ya ya cigaba da aikin sa, kuma har yanzu ya na bin duk umurnin da sabon ubangidan sa ya ba shi.
A baya dai rahotanni sun ambato Sule Lamido ya na cewa, sakin Sambo Dasuki da Ministan shari’a ya sa aka yi ya nuna cewa tun farko ba zargin satar kudi ta sa aka kama shi ba.
Tsohon
gwamnan ya cigaba da cewa, tsare Knar Sambo Dasuki da aka yi bay a da alaka da
badakalar kudin makamai na Dala biliyan 2 da miliyan 100.