Wakiliyar Asusun Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya Cristian Munduate, ta bukaci Gwamnatin Nijeriya ta yi amfani da dokokin da su ka dace domin gurfanar da ‘yan bindigar da su ka aikata ta’asar cin zarafin Bil Adama.
Cristian ta yi kiran ne, yayin wani taron tattaunawa da manema labarai na shirye-shiryen bikin ranar jin-kai ta duniya a Maiduguri.
UNICEF ya yi nuni da cewa, abu ne da ba za a amince da shi ba cewa gwamnatoci ba su dauki tsattsauran mataki a kan wadanda su ka sace daliban makaranta da kashe mata da malamai da kuma yi wa kananan yara mata fyade ba.
Cristian Munduate, ta bukaci a karfafa tsarin shari’a yadda ya kamata, sannan ta yi gargadin a daina wannan aika-aika, ta yadda yara za su iya zuwa makarantu ba tare da fargabar sace su ko yi masu fyade ba.
You must log in to post a comment.