Home Labarai Yaƙi Da Ambaliyar Ruwa: Nijar Ta Ware Dala Miliyan Uku

Yaƙi Da Ambaliyar Ruwa: Nijar Ta Ware Dala Miliyan Uku

60
0
Jigawa flood1
Jigawa flood1

Gwamnatin soji ta Jamhuriyar Nijar ta ware kuɗi dalar Amurka miliyan uku domin yaƙi da ambaliyar ruwa da ta addabi ƙasar,

wadda zuwa yanzu ta kashe aƙalla mutum 217, kamar yadda tashar RTN Tele Sahel ta gwamnatin ƙasar ta ruwaito.

Shugaban mulkin sojin, Birgediya Janar Abdourahmane Tiani ya bayyana a taron Majalisar Zartarwar ƙasar a ranar 22 ga watan Agusta cewa,

za a yi amfani da kuɗin, wanda aka ciro daga baitul malin ƙasar ne domin yaƙi da ambaliya domin kare ƴancin kasar.

Marka-markar ruwan sama a ƙasar ya jawo ambaliyar ruwa, wadda ta shafi sama da mutum 353,000, sannan ta lalata gidaje da manyan hanyoyi.

Ƙididdiga ta baya-baya ta nuna cewa ruwan ya janye mutum 108, sannan wasu 109 sun mutu lokacin da gini ya rufto musu.

Ɗaruruwan mutane sun samu rauni, sannan dubbai sun rasa muhallan su a sanadiyar ambaliyar da ta addabi ƙasar.

Ma’aikatar Ayyukan Jin-ƙai ta Nijar ta samu agaji daga Aljeriya a ranar 22 ga Agusta domin agaza wa waɗanda ibtila’in ya shafa.

Leave a Reply