Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Wutar Lantarki: Minista Ya Ba Da Umarnin Dawo Da Wutar Kano

Ministan Wutar Lantarki Abubakar Aliyu, ya bada umarnin a
maida wutar da aka yanke wa Kamfanin Wutar Lanarki na
jihar Kano KAEDCO saboda taurin bashi.

Abubakar Aliyu, ya umarci Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa TCN ya maida wa KAEDCO da kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Kaduna wutar ne daga karfe 12 na daren Litinin 1 ga watan Mayu na shekara ta 2023.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Kasa ta fitar, ta ce za a maida wa kamfanonin wutar ne bayan ministan ya sanya baki, da nufin rage wahalar da rashin wutar ya jefa masu amfani da ita.

Ministan, ya bukaci kamfanin TCN ya kara wa kamfanonin da sauran wadanda ya ke bi bashi kwanaki 60 domin su samu su biya.

Ya ce idan wa’adin ya cika kamfanin zai katse layukan duk masu taurin bashin, don haka ya kamata su yi amfani da kwanakin da aka bada wajen sauke nauyi su cika alkawari.

Exit mobile version