Home Labarai Wike Ya Ce Jirgin Ƙasan Birnin Abuja Zai Ɗauki Fasinjoji Kyauta

Wike Ya Ce Jirgin Ƙasan Birnin Abuja Zai Ɗauki Fasinjoji Kyauta

23
0
Wike 3
Wike 3

Ministan Abuja, Wike, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da fara ɗiban fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa na birnin tsawon wata biyu.

Wike ya bayyana haka ne yayin taron bayyana ayyukan da ma’aikatu ke yi shekara ɗaya da kafa gwamnatin ta Tinubu.

A makon gobe ne dai ake sa ran ƙaddamar da jigilar fasinjoji ƙwaryar birnin Abujan.

Ya ce shugaban ƙasa zai ƙaddamar da layin dogon ranar 27 ga watan Mayu, sannan a fara jigilar mutane kyauta tsawon wata biyu.

Sai dai hukumar kula da birnin Abuja ta ce yanzu an mayar da ranar ƙaddamarwar zuwa 29 ga wata.

Ministan ya ce mutane da yawa na cewa gwamnatin baya ta ƙaddamar da shi. Mu ba maganar ƙaddamar da gine-gine muke yi ba, fara aikin jigilar mutane za mu ƙaddamar.

Leave a Reply