Home Labaru Wata Sabuwa: ‘Yan Majalisar Kano Sun Yi Wa Kan Su Dokar Yanke...

Wata Sabuwa: ‘Yan Majalisar Kano Sun Yi Wa Kan Su Dokar Yanke Talauci

356
0

Shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano Kabiru Alhassan Rurum, ya ce sabuwar dokar da su ka gabatar ta ba shugaban majalisa da mataimakin sa fansho na har abada za ta taimaka wajen rage wa ‘yan siyasar da su ka sauka daga mukaman su radadin wahala.

Majalisar dokoki ta jihar dai ta gabatar da sabon kudurin dokar ne a ranar Talatar da ta gabata, wanda zai ba shugaban majalisar da mataimakin sa fansho na tsawon rayuwar su da kuma zuwa kasashen waje duba lafiyar su duk shekara.

Rurum ya shaida wa manema labarai cewa, an yi sabuwar dokar ne don a rage cin hanci da rashawa da kuma hana ‘yan siyasa shan wahala yayin da ba su kan mukamai.

Baya ga ba su fansho na har abada, sabuwar dokar za ta kuma ba su damar mallakar sabbin motoci duk bayan shekara hudu, sannan za su samu damar zuwa kasashen waje domin duba lafiyar su, ko kuma duk asibitin da ya yi masu a fadin Nijeriya tsawon rayuwar su.

Leave a Reply