Shugaban rundunar atisayen Operation Hadarin Daji Manjo Janar Jide Ogunlade, ya ja hankalin gwamnati cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun fara hada kai da ‘yan bindigar da su ka addabi jihar Zamfara.
Janar Ogunlade ya bayyana wa manema labarai haka ne a herkwatar Sojoji a birnin Gusau na jihar Zamfara.
Yace ‘yan Boko Haram sun fara shiga cikin ‘yan bindigar dake kai hare-hare a jihar Zamfara, kuma sun fara ganewa ne ta rawanin da su ke daurawa mai dauke da rubutun jihadi.
Manjo Ogunlade ya cigaba da cewa, tun da ‘yan Boko Haram sun fara sauya salo za su fara sauya na su, amma idan su ka kara yawa za a ba gwamnatin tarayya shawarar alamta su a matsayin ‘yan ta’adda. A karshe ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, duk sojojin da ke karkashin shi za su gudanar da ayyukan su bisa tsarin doka, musamman wajen kare rayuka.