Home Home Wata Sabuwa: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fasinjan Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna

Wata Sabuwa: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fasinjan Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna

65
0
‘Yan bindiga sun kashe daya daga cikin kubutattun Fasinjojin Jirgin Kasan da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda ya rasa ran shi a kan hanyar Funtua zuwa Gusau yayin da ke komawa garin su da ke jihar Kebbi.

Wanda lamarin ya rutsa da shi dai ba a bayyana sunan shi ba har yanzu, amma ya na daga cikin wadanda su ka shafe tsawon watanni shida a hannun masu garkuwa da mutane, tun lokacin da su ka yi garkuwa da su a ranar 28 ga watan Maris na shekara ta 2022.

An dai kashe mutumin ne a kan hanyar sa ta komawa garin su, tare da makusantan sa da ahlin sa bayan sun sake haduwa biyo bayan mika masu shi da gwamnatin jihar Kaduna ta yi bayan sun samu kubuta a makon da ta gabata.

Wata majiya ta ce, daya daga cikin makusantan marigayin da ke tuka motar, an yi garkuwa da shi zuwa wani wurin da har yanzu ba a sani ba.

Majiyar ta ce, ‘yan bindigar sun harbi mamacin ne a tsakiyar Kai, inda ya mutu ‘yan sa’o’i bayan an hanzarta kai shi babban asibitin Tsafe, kuma tunin an yi masa Jana’iza a garin su kamar yadda addinin musulunci ya tanada.