A ranar litinin da ta gabata ne, wata matar aure mai suna Rabi Shamsuddeen ta kashe mijin ta da wuka a karamar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
Rabi da mijin ta Shamsuddeen Salisu dais u na zaune ne a kauyen Danjanku-Tasha da ke karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.
Makwafta da su ka bayyana wa ‘yan sanda abin da ya faru sun shaida cewa, sun rika jin Ihun Sahamsuddeen yana kira da azo a taimake shi a kuma kai ma shi dauki, amma da zuwa sun iske an datse kyauren gidan da kwado daga ciki.
Bayan an haura Katanga ne aka iske mijin kwance a cikin jini, yayin da matar ke tsaye a kan sa da sharbebiyar wuka duk jini ta na kallon su.
Kakakin
‘yan sanda na jihar Katsina Gambo Isah ya shaida wa manema labarai cewa tuni
‘yan sanda sun fara bincike, kuma da zarar ta kammala za a gurfanar da Rabi a
gaban kotu.