Home Home Wata Sabuwa: Wani Bom Ya Fashe a Wani Gidan Barasa Da Ke...

Wata Sabuwa: Wani Bom Ya Fashe a Wani Gidan Barasa Da Ke Jihar Yobe

179
0

Mutum ɗaya ya rasa rayuwar sa, yayin da wasu akalla bakwai su ka jikkata, sakamakon fashewar wani abin fashewa a wani gidan barasa da ake kira Gidan Amarya a jihar Yobe.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a garin Gashua, Hedkwatar karamar hukumar Bade, a jihar dake arewa maso gabashin Najeriya.

Mazauna garin sun ce, an ji ƙarar fashewar abin a duk sassan Gashua da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Lahadin da ta gabata bayan sallar Tarawihi.

Wani mai shago da ke kusa da gidan barasar Abdu Sherrif, ya ce mutane da yawa sun yi takan su domin tsira da rayuwar su.

Shugaban ƙaramar hukumar Bade Sanda Kara Bade, ya ce gwamnatin sa ta tura jami’an tsaro zuwa wurin, ya kuma bada umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin fashewar.

Ya ce tuni an ɗauke mutanen da su ka jikkata sanadiyyar lamarin zuwa Asibitin gwamnati domin kula da lafiyar su.

Leave a Reply