Home Labaru Wata Sabuwa: Masu Ruwa Da Tsaki A APC Sun Nemi Buhari Ya...

Wata Sabuwa: Masu Ruwa Da Tsaki A APC Sun Nemi Buhari Ya Tsige Abba Kyari

511
0

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC sun mamaye fadar Shugaban kasa, inda su ka bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari.

Mutanen, sun kuma bukaci Shugaba Buhari ya karbi ragamar gwamnatin sa daga hannun na kewaye da shi, yayin da ya fara mulki a zango na biyu.

Wasu daga ciki allunan da ke hannun mutanen, su na dauke da rubutu daban-daban da ke cewa, ‘ya zama dole Abba Kyari ya tafi’, ‘Ya zama dole Buhari ya karbi ragamar mulki’, ‘Muna son sabbin mashawarta tsofaffin da su ka shafe sama da shekaru 40 a mulki ba’.

Jagoran kungiyar Dakta Symeon Chilagorom ya yi korafin cewa, ‘yan Nijeriya sun zabi shugaba Buhari ne ba Mamman Daura ko Sama’ila Isah Funtua ko Abba Kyari ba, ya na mai jadadda cewa ‘yan Nijeriya ba za su lamunci abin da ya faru karo na farko ya sake maimaita kan sa ba.

Leave a Reply