Home Labaru Ilimi Wata Sabuwa: Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Komawa Yajin Aiki

Wata Sabuwa: Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Komawa Yajin Aiki

375
0

Kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya ASUU, ta yi barzanar shiga wani sabon yajin aikin sai-baba-ta-gani, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya na rashin cika alkawarin yarjejeniyar da su ka kulla a baya.

ASUU ta ce kada a zargi ‘ya’yan ta a duk lokacin da su ka durkyusar da harkokin karatu a jami’o’in Nijeriya, sakamakon yadda gwamnatin tarayya har yanzu ta gaza wajen cika alkawarin yarjejeniyar da ta kulla a baya.
Shugaban kungiyar na kasa Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana haka, yayin wata ganawar musamman da ya yi da manema labarai a Abuja.

Ogunyemi, ya yi tsokaci dangane da alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi wa kungiyar ASUU na ba ta Naira biliyan ashirin da biyar a bana, kamar yadda Ministan ilimi Adamu Adamu ya bada tabbaci.

Leave a Reply