Home Labaru Wata Sabuwa: Karuwanci Ba Haramun Ba Ne A Abuja – Kotu

Wata Sabuwa: Karuwanci Ba Haramun Ba Ne A Abuja – Kotu

946
0

Wata kotu da ke zama a Abuja ta yanke hukuncin cewa Karuwanci ba laifi ba ne, kasancewar babu wata doka da ta haramta shi a Nijeriya.

Mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun da ke Abuja, ta nemi a biya diyya ga mata 16 da aka kama bisa tuhumar su da laifin karuwanci a shekara ta 2017.

Wannan dai shi ne karo na farko da wata kotu a Nijeriya ta yanke hukunci kan halascin Karuwanci.

Lauyan da ke kare matan Babatunde Jacob ya shaida wa manema labarai cewa, kotun ta ce jami’an tsaro sun keta hakkin wadanda ya ke karewa, kasancewar sun kutsa cikin gidajen su su ka kama su bisa zargin karuwanci.

Masana shari’a a Nijeriya dai su na ganin hukuncin zai iya yin tasiri ga ‘yan Nijeriya, wadanda su ka fi kowace al’umma yawa a nahiyar Afirka.

Idan dai ba a manta ba, yayin wani samame a cikin watan Mayu na shekara ta 2019, an kama sama da mata 60 bisa zargin yin karuwanci a birnin Abuja.

Leave a Reply