Home Labaru Wata Sabuwa: Hukumar Raba Hasken Lantarki Za Ta Fara Tilasta Sayen Mita...

Wata Sabuwa: Hukumar Raba Hasken Lantarki Za Ta Fara Tilasta Sayen Mita A Kan Naira 36,991.50

270
0

Hukumar Raba Hasken Lantarki ta Kasa NERC, za ta fara tilasta yin amfani da mita daga ranar 1 ga Mayu na shekara ta 2019.

Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar Usman Arabi ya bayyana haka, ya na mai cewa za a fara raba mita ga jama’a a karkashin wani tsari da gwamnatin tarayya ta bullo da shi.

Ya ce dokar raba hasken lantarki ta Sashe na 4 (3), ya bukaci kowa ya yi amfani da mita domin a rage matsalar da ake fuskanta.

Arabi ya ce, masu amfani da wutar lantarki daga Kamfanin AEDC na Abuja da kuma JEDC na Jos, za su iya samun mita bayan kwanaki goma kacal da biyan kudin mitar.

Ya ce za a karbi naira 36,991 daga wanda zai daura layin wuta daya a gidan sa, wanda zai daura layi biyu kuma zai sayi mita mai layi uku a kan kudi naira 67,055.

Arabi ya kara da cewa, mitar ta yi tsada ne saboda an hada farashin ta har da ladar aikin kai wa mutum har gida, da daurawa, da kuma ladar zuwa a gyara ma shi idan ta lalace, ko kuma a sauya ma shi wata idan ba za ta iya gyaruwa ba.