Gwamnatin jihar Filato ta cire masarautun Jos ta arewa da kuma Riyom daga karkashin gamayyar masarautar Jos da Sarkin Jos Buba Jacob ke jagoranta.
Mutanen jihar da dama dai na ganin lamarin a matsayin wani yunkuri na takaita karfin ikon sarkin. A cikin watan Agustan da ya gabata ne, gwamna Simon Lalong ya kirkiri wasu sabbin hakimai, yayinda ya daga darajar masarautun Jos ta arewa da Riyom.