Takaddama ta barke a asibitin koyarwa na jami’ar Jos, yayin da dalibai mata musulmai da ake ba horo a asibitin, su ka yi zargin cewa ana tursasa su cire hijabi a sashen kiwon lafiya da ke asibitin.
Fusatattun daliban sun bayyana wa manema labarai cewa, shugaban sashen kiwon lafiyar ya na ci masu mutunci, inda su ka ce ya ba su zabin ko su bar makarantar, ko kuma su bar gashin kan su a bude.
Tuni dai wata kungiyar matasa ta aike wa babban daraktan asibitin Farfesa Edmund Banwat wasika mai dauke da sa hannun shugaban ta Buhari Ibrahim Na Shehu, inda ta ce matakin da sashen kiwon lafiyar ya dauka cin zarafin dalibai musulmai mata ne.
Na Shehu, ya ce wannan ya na daga cikin abubuwan da su ka saba ma dokar kungiyar ma’aikatan jinya ta kasa, wadda ta ba dalibai musulmai da kiristoci damar sanya mayafai kamar yadda addinan su su ka tanada.Sai dai a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, hukumar asibitin ta bayyana zargin a matsayin karya.