Home Labaru Wata Sabuwa: An Fara Yi Wa ‘Yar Jaridar Da Ta Yi Wa...

Wata Sabuwa: An Fara Yi Wa ‘Yar Jaridar Da Ta Yi Wa Malaman Jami’o’i Tonon Silili Barazana

521
0
Kiki Mordi

‘Yar jaridar kafar yada labarai ta BBC da ta yi badda-kama domin ta tona wa malaman jami’a asiri a kan abin da su ke yi na fasikanci da dalibai kafin su ba su maki Kiki Mordi, yanzu haka ta fara samun barazanar kisa daga wajen mutanen da tonon sililin bai yi wa dadi ba.

Kiki, wadda ta ce ita kan ta ta shiga wannan hali, inda malami ya bukaci ya yi fasikanci da ita a lokacin da ta ke jami’a.

Ta ce ta fara samun barazana a kan binciken da ta yi, inda aka bayyana ta da kuma wasu ‘yan’uwan ta ‘yan jarida mata a lokacin da su ke daukar bidiyon wasu malaman jami’a na Legas da wasu a kasar Ghana a boye, inda malaman ke amfani da matsayin su su na fasikanci da dalibai mata kafin su ba su maki.

Sai dai ta ce ita bata damu da wannan barazana da ake yi mata ba, saboda ta san cewa BBC ta na karfafa tsaro ga dukkan ma’aikacin da su ka dauka aiki.

Ta ce ta ji dadi matuka da ganin irin sauyin da ake samu tun bayan fitar bidiyon, ta na mai tabbatar da cewa, daya daga cikin malaman jami’ar Legas an kama shi dumu-dumu ya na neman ya yi fasikanci da wata daliba da ta je neman gurbin karatu.

Leave a Reply