Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Wasu ‘Yan Siyasa Na Shirin Guduwa Kafin 29 Ga Watan Mayu – EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce wasu ‘yan
siyasa da ta ke zargi da rashawa su na ƙoƙarin ficewa daga
Nijeriya kafin su sauka daga mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

EFCC ta bayyana haka ne, yayin da ta ke maida wa gwamna Matawalle na jihar Zamfara martani game da zargin da ya yi wa shugaban ta Abdulrasheed Bawa cewa ya nemi rashawar dala miliyan biyu a hannun sa.

Wata sanarwa da hukumar EFCC ta fitar, ta ce idan har Matawalle da gaske ya ke yi, ya kamata ya daina ɓaɓatu ya gabatar da hujja ƙarara a kan zargin da ya ke yi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, hukumar na ankarar da al’umma cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ake zargi da cin hanci da rashawa, wadanda ke shirin ficewa daga Nijeriya kafin ranar 29 ga watan Mayu.

Exit mobile version