Gamayyar wasu ƙungiyoyi a ƙarƙashin kungiyar yaki da cin
hanci a Nijeriya MACIN, ta yi kira ga hukumar shige da fice
ta ƙasa da ‘yan sandan kasa da kasa su sa ido a kan tsohon
gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje don kada ya
gudu ya bar Nijeriya.
Kungiyar ta bayyana haka ne, yayin tattaunawa da manema labarai a sakatariyar ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa a birnin Kano.
Shugaban ƙungiyar Kabiru Sa’idu Dakata, ya buƙaci hukumomin biyu su sa ido a kan Ganduje, saboda ya na ɓoyewa a bayan Shugaba Tinubu don kada a kama shi, inda daga bisani zai yi ƙoƙarin sulalewa daga Nijeriya.
Ƙungiyar, ta kuma yi kira ga Ganduje ya mutunta doka ya kai kan sa wajen hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano domin a bincike shi.
Da ya ke martani a kan kiran da ƙungiyar ta yi, tsohon kwamishinan watsa labarai a gwamnatin Ganduje Malam Muhammad Garba, ya yi fatali da kiran da ƙungiyar ta yi na Shugaba Tinubu ya nesanta kan sa da tsohon gwamnan.