Home Labaru Wasikar Tuhuma: Sarki Sanusi Ya Maida Wa Ganduje Martani

Wasikar Tuhuma: Sarki Sanusi Ya Maida Wa Ganduje Martani

468
0

Majalisar masarautar Kano, ta maida martani ga wasikar tuhuma da gwmanatin Kano ta aike wa Sarki Muhammadu Sanusi na II ta neman ya yi bayani dangane da zargin kashe sama da Naira biliyan uku bayan ya zama Sarkin Kano.

Martanin dai ya na cikin wata wasika ne da majalisar ta aike wa gwamnati ta ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano.

Wasikar ta ce, abin da Sarki Sanusi ya gada a asusun masarautar shi ne Naira biliyan daya da miliyan dari takwas da casa’in da uku.

Wasikar, wadda mukaddashin masarautar Kano Abba Yusuf ya sanya wa hannu, ta ce ba sarkin Kano ke da alhakin yin bayani a kan yadda aka kashe kudaden masarautar ba, tun da ba shi ne mai kula da kudin masarautar ba.

Masarautar ta kuma gode wa gwamnati saboda ba ta damar yin bayani akan zarge-zargen da ke kunshe a rahoton hukumar yaki da cin hanci da rashawa, da ma yin cikakken bayani a kan yadda aka kashe kudaden.

Leave a Reply