Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi, ta kama wani matashi bisa zargin shi da kokarin kisan kai ta hanyar banka ma wata karamar yarinya wuta.
Matashin dai ya zargi yarinyar da cewa ita mayya ce, shi ya sa ya cinna mata wuta bayan takun-sakar da ya shiga tsakanin su.
A wata sanarwar manema labarai da kakakin rundunar Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya ce an kama mutumin ne bisa zargin yunkurin kisan kai da azabtar da karamar yarinyar.
Wanda ake zargin ya bayyana abin da ya faru a matsayin tsautsayin da ya rutsa da Hafsat Bala a gidan sa da ke yankin Rafin Albasa a Bauchi.
A Wakili, ya ce lokacin da ‘yan sanda su ka samu rahoton faruwar lamarin, sun garzaya bisa jagorancin babban baturen yanki domin ceto yarinyar zuwa asibitin koyarwa na Tafawa Balewa.