Home Labaru Kasuwanci Wahalar Fetur: Manyan ’Yan Kasuwa Sun Sayo Lita Miliyan 300

Wahalar Fetur: Manyan ’Yan Kasuwa Sun Sayo Lita Miliyan 300

109
0
Huub Stokman
Huub Stokman

Kungiyar Manyan Dillalan Man Fetur ta kasa (MEMAN) ta
kammala shirin shigo da manyan jiragen ruwa guda takwas
masu dauke da litar mai sama da miliyan 300 domin magance
karancin man da ake fama da shi a halin yanzu.

Shugaban MEMAN, Huub Stokman ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai domin magance karancin man fetur ɗin da ake fama da shi a kasar. Stokman wanda ya tausaya wa ’yan Najeriya kan bacin rai da wahalar da suke fuskanta, ya ce, “Babban abin da muka sa a gaba a matsayinmu na MEMAN shi ne dawo da kwanciyar hankali da tabbatar da samar da man fetur a ɗaukacin gidajen mai a faɗin Najeriya cikin gaggawa.


Mambobinmu za su shigo da jiragen ruwa takwas masu ɗauke da lita sama da miliyan 300 na fetur a wannan makon, wanda ya zarce abin da da muka saba ɗaukowa. Shugaban manyan ’yan kasuwar ya ɗora alhakin halin da ake ciki a kan abubuwa da dama, kamar rashin kyawun yanayi a teku da kuma wasu al’amurra.

Leave a Reply