Home Labaru Wa’adin Mulki: Sanata Ekweremadu Ya Maida Motocin Ofishin Sa

Wa’adin Mulki: Sanata Ekweremadu Ya Maida Motocin Ofishin Sa

309
0
Sanata Ike Ekweremadu, Tsohon Mataimakin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Tsohon mataimakin Mataimakin Shugaban majalisar dattawa a majalisa ta takwas Sanata Ike Ekweremadu ya maida motocin sa na aiki.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Litinin da ta gabata ne, aka yi ta rade-radin cewa Ekweremadu ya ki maida motocin sa na aiki duk da wa’adin mulkin su ya kare.

Sai dai wata majiya ta kusa da tsohon Sanatan ta bayyana cewa, an maida motocin ne a daren Litinin bayan an yi masu garambawul sannan aka wanke su.