Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankuna su daina bayar da sabon kuɗi ga kwastomomin da suka shiga cikin banki domin karɓar kuɗi.
CBN ya ce kamata ya yi bankunan su saka sabbin kuɗin cikin na’urorin su na cirar kuɗi wato ATM, domin tabbatar da cewa kuɗin ya shiga hannun jama’a gabanin ranar wa’adin 31 ga watan da muke ciki da babban bankin ya saka na daina amfani da tsohon kuɗin.
Rahotonni sun ce babban bankin ya umarci bankunan su gaggauta aiwatar da wannan umarni.
A watan Oktoban da ya gabata ne Babban Bankin na Najeriya CBN, ya sanar da matakin sauya fasalin kuɗaɗen ƙasa, tare da umartar mutane su mayar da tsofaffin kudaɗen banki domin sauya musu da sababbi.