Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Villarreal Ta Samu Gurbin Shiga Zagaye Na 16

Villarreal ta samu gurbin zuwa zagayen ‘yan 16 na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a matsayin ta biyu a rukunin F bayan da ta doke Atalanta a karawar da suka yi a Bergamo wanda aka dage tun farko.

Arnaut Danjuma ne ya baiwa maziyartan jagoranci a minti na uku a wasan da aka dage ranar Laraba saboda tsananin dusar kankara.

Etienne Capoue ya kara ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci kuma Danjuma ya sauya labarin zuwa ci 3-0 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Sai daga bisani Ruslan Malinovskyi da Duvan Zapata suka ramawa Atalanta, kwallaye biyu, amma aka tashi 3-2.

Da wannan sakamako Villarreal zata kasance cikin ‘yan zagayen 16, yayin da Atalanta za ta yi kokarin zuwa gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa.

Exit mobile version