Home Labaru Venezuela: Juan Gaido Na Shirin Kawo Karshen Mulkin Maduro

Venezuela: Juan Gaido Na Shirin Kawo Karshen Mulkin Maduro

611
0
Venezuela's National Assembly head Juan Guaidó waves during a mass opposition rally, during which he declared himself the country's acting president on Jan. 23

Shugaban ‘yan adawa na kasar Venezuela Juan Gaido ya bayyana cewa , ya kama hanya ko kuma shiga mataki na karshe don kawo karshen shugabancin Nicolas Maduro a kasar.
Magoya bayan shugaban yan adawa sun gudanar da zanga-zanga, inda Juan Gaido ya bayyana takaicin sa dangane da rashin wuta dama karancin kayakin more rayuwa da yan kasar ke fama da shi tsawon lokaci.
Juan Gaido ya bayyana cewa shirye yake ya kawo karshen mulkin Nicolas Maduro, yayinda Shugaba Maduro ya bayyana fatan sa na ganin kasashen Mexico da Uruguay ,Bolivia da wasu kasashen yankin Caraibe sun tsoma bakin su a batun sulhunta bangarorin biyu cikn dan karamin lokaci.