Home Labarai Umurnin Samar Da Abinci: Hukumar Kwastam Ta Saki Motoci 15 Na Hatsi...

Umurnin Samar Da Abinci: Hukumar Kwastam Ta Saki Motoci 15 Na Hatsi Da Aka Kama

36
0

Hukumar Kwastam shiyyar Sokoto da Zamfara, bisa bin umarnin da shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bayar na inganta samar da abinci, ta bayar da izinin sakin manyan motoci 15 da aka kama maƙare da hatsi ga masu su a ranar 12 ga Maris, 2024.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a shiyyar, ta buƙaci ‘yan kasuwa su gaggauta sayar da hatsin a kasuwannin Najeriya, yana mai jaddada ƙudurin hukumar na yaki da ayyukan fasa-kwauri.

Bugu da kari, Kwanturola Kamal ya sanar da kokarin hadin gwiwa tare da hukumar tattara bayanan sirri na Kwastam (CIU) da kuma kungiyar hadin gwiwa (JBPT) domin sanya ido kan yadda ake rarraba wadannan hatsi a kasuwannin cikin gida, tare da tabbatar da cewa ba za su samu hanyar fita daga ƙasar ta hanyoyin fasakwauri ba.

A nasa ɓangaren, sakataren kungiyar masu sayar da hatsi ta Sokoto Dahiru Ladan, ya nuna jin dadin sa ga shugaba Tinubu bisa tausayawar da ya yi, ya kuma tabbatar wa jama’a cewa ƙungiyar za ta tabbatar da cewa an sayar da hatsin a kasuwannin Najeriya ne kadai.

Leave a Reply