Home Labaru Tuwo Na Mai Na: Ahmed Lawan, Omo-Agege Sun Karbi Shugabancin Majalisar Dattawa

Tuwo Na Mai Na: Ahmed Lawan, Omo-Agege Sun Karbi Shugabancin Majalisar Dattawa

722
0

An bayyana Sanata Ahmed Lawan na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban majalisar dattawa da kuri’u 79, inda ya kada Sanata Ali Ndume da ya samu kuri’u 28.

Hakan kuwa ya na nufin cewa, Sanata Ahmed Lawan mai wakiltar mazabar Yobe ta Arewa ya yi nasara da tazarar kuri’u 51, inda nan take Sanata Ali Ndume ya taya shi murna.

A wani bangaren kuma, Sanata Omo-Agege ya yi nasarar zama mataimakin shugaban majalisar dattawa, inda ya samu kuri’u 68, yayin da abokin karawar sa Sanata Ekweremadu ya samu kuri’u 37.

Zaben dai ya haifar da ce-ce-ku-ce, musamman bayan jam’iyyar APC ta nuna goyon bayan ta ga takarar Sanata Ahmed Lawan, lamarin da ya sa jam’iyyar PDP ta goyi bayan Sanata Ali Ndume.

Leave a Reply