Home Home Tukwicin Biyayya: PSG Za Ta Biya Mbappe Euro Miliyan 60

Tukwicin Biyayya: PSG Za Ta Biya Mbappe Euro Miliyan 60

1
0

Rahotanni daga birnin Paris na cewa akwai yiwuwar PSG za ta biya dan wasan ta Kylian Mbappe kudaden da yawan su ya kai euro miliyan 60 a matsayin tukwicin yabawa da biyayya ko amintakar da ke tsakanin su.

Bayanan sun ce kungiyar ta París Saint Germaine za ta biya tauraron na ta makudan kudaden ne, muddin bai raba gari da ita ba har zuwa ranar 1 ga watan Agusta, duk da cewar dangantakar da ke tsakanin su ta yi rauni matuka, biyo bayan kin tsawaita yarjejeniyar sa da ya yi da ke shirin karewa a 2024.

Yanzu haka dai kungiyoyi da dama ne ke neman kulla yarjejeniya da dan wasan na Faransa, tuni kuma kungiyar Al-Hilal ta Saudiya ta gabatar da tayin euro miliyan 300 wanda PSG ta karba.

Sai dai Mbappe ya dage kan cigaba da zama a kungiyar ta sa, har zuwa lokacin da yarjejeniyar sa za ta kare.