Home Home Tukur Mamu Ya Ƙi Amsa Tuhuma

Tukur Mamu Ya Ƙi Amsa Tuhuma

13
0

Tsohon mai shiga tsakani wajen tattaunawa da ‘yan ta’adda Tukur Mamu, ya ƙi amsa tuhumar laifuffuka 10 da Gwamnatin Tarayya ke zargin sa da aikatawa.

Ofishin Babban Lauyan Nijeriya dai ya gurfanar da Mamu a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin taimaka wa ‘yan ta’adda.

A ranar 13 ga watan Satumba na shekara ta 2022, Mai Shari’a Nkeonye Maha ta wata kotun tarayya, ta ba hukumar tsaro ta farin kaya SSS izinin tsare Tukur Mamu na tsawon kwanaki 60 domin ta kammala bincike a kan sa.

Darakta mai shigar da kara na gwamnatin tarayya M.B. Abubakar ne ya sanya hanya a takardar tuhume-tuhumen da ake yi wa Tukur mamu, wadanda su ka hada da karɓar kuɗin fansa Dala dubu 120 a madadin Boko Haram daga hannun ‘yan’uwan fasinjojin da aka yi garkuwa da su a jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna.