Home Labarai Tu’annati: Hukumar NDLEA Ta Kama Manyan Dilolin Wiwi Da Ƙwaya

Tu’annati: Hukumar NDLEA Ta Kama Manyan Dilolin Wiwi Da Ƙwaya

81
0
NDLEA (2)
NDLEA (2)

Hukumar hana sha da Fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta kama manya-manyan dilolin muggan miyagun ƙwayoyi da wiwi a jihohin Najeriya. 

NDLEA, ta gano wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta ƙasa da ƙasa a sassan Najeriya da ke da alaƙa da Afirka ta Kudu da kuma ƙasar Thailand.

Aƙalla mambobin ƙungiyar biyar ne aka kama a wani samame na tsawon makonni biyu da jami’an leken asirin suka gudanar a jihohin Legas, Abia da Anambra, biyo bayan ƙwace haramtattun kwayoyi a shalkwatar shigo da kaya NAHCO dake filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Ikeja a Jihar Legas.

Jami’an NDLEA da ke bincike a kan hanyar Abuja zuwa Abaji a ranar Laraba 1 ga watan Mayu, sun kama wata tankar iskar gas mai tsawon mita 40 mai lamba RBC 77XG, bayan bincike da aka gudanar an samu buhunan tabar wiwi 511 mai nauyin kilogiram 4,752.

An ɗakko buhunan wiwi ɗin ne daga jihar Ondo za a kawo Abuja domin ci gaba da rarrabata ga mabuƙata.

Jami’an hukumar sun ce sun kama waɗanda ake zargin kuma suna hannunsu.

Leave a Reply