Home Home Tu’ammali Da Muggan Ƙwayoyi Da ‘Cutar Damuwa’ Na Damun Wasu Sojoji –...

Tu’ammali Da Muggan Ƙwayoyi Da ‘Cutar Damuwa’ Na Damun Wasu Sojoji – Lagbaja

2
0

Babban Hafsan Askarawan Nijeriya Taoreed Lagbaja, ya ce Rundunar Sojojin za ta cigaba da shirya horarwa ga zaratan ta domin ƙara zaburar da su wajen ƙara zage damtse su fuskanci ayyukan da ke gaban su.

Lagbaja ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke jawabin buɗe taron kwana ɗaya da Rundunar Sojojin runduna ta 6 da ke Fatakwal ta shirya.

Janar Lagbaja ya ce Nijeriya ta na fuskantar matsaloli da ƙalubalen tsaro daban-daban, waɗanda su ka haifar da ɗora wa sojoji nauyin daƙile su.

Ya ce domin ganin an cimma biyan buƙatar magance matsalolin, Sojojin Nijeriya za su sake nazarin salo da dabaru, da fasaha da tsare-tsaren yadda za a ga bayan miyagu da maɓarnata da abokan gaba.

A karshe ya ce abin damuwa a gare su shi ne, ganin yadda tu’ammali da ƙwayoyi masu bugarwa ke ƙara tasiri a cikin sojojin Nijeriya, da kuma matsalar Tsananin Damuwa Bayan Kasancewa a Filin Daga.