Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsokaci: Mahimmancin Tsaro Da Yaki Da Cin Hanci – Dan Agbese

Aliyu Abdullahi Gora II Ya Fassara Ya Kuma Zai Kuma Karanto

A yadda tabarbarewar tsaro ta hana gudanar da bukukuwan sallah a jihar Katsina, babu wani shugaban kasa, komai kwarewar shi, duk irin kasancewar shi dan kishin kasa, da zai iya shawo kan dukkan matsalolin da kasar shi ke fuskanta.

Idan har ba a iya magance matsalolin da su ka shafi sata da kisan kai, tun bayan da Annabi Musa A.S ya karbo hukunce-hukunce goma daga Dutsin Siniin tsawon dubannin shekarau da su ka gabata ba, babu ta yadda shugaban Nijeriya zai iya magance dukkan matsalolin da su ka hada da rikita-rikitar siyasa, da tattalin arziki, da sauran al’amurran da su ka shafi rayuwar al’aumma a cikin shekaru takwas.

Abin da kawai zai iya yi shi ne, ya zabi wata matsala, wadda ita ce ta fi ci ma al’umma tuwo a kwarya ya magance ta iyakar karfin shi.

Na tabbata, shugaba Muhammadu Buhari ya tsinci kan shi a cikin irin wannan dambarwa a wa’adin mulkin shi na biyu.

Yayin da ya yi alkawarin kawo Canji a shekara ta 2015, matsalar da ya ke ganin ita ya kamata a gaggauta magancewa, ita ce matsalar cin hanci da rashawa, kuma zakakuran ma’aikatan da aka rataya wa wannan nauyi har yau ba su yi kasa a gwiwa ba.

Sai dai ina tababar, idan har yanzu shugaban kasa ya na kallon wannan a matsayin ita ce gagarumar matsalar da ta addabi kasar nan, duba da matsananciyar matsalar tabarbarewar tsaro, da matsanancin talauci, da kuma dimbin jahilcin da ake mafa da shi a yau.

Tabbas, yaki da cin hanci da rashawa abu ne mai matukar mahimmanci, domin ya kassara kasar mu, ya kuma lalata kimar mutanen mu a idon duniya, ta yadda a duk lokacin da aka ambaci sunan Nijeriya a wata kasa, abin da ke fara zuwa a zukatan mutane shi ne cin hanci, amma a yau, an daina yi wa ‘yan Nijeriya kallon uku-kwabo a kasashen ketare.

Sai dai a shekaru hudun da su ka gabata na shugabancin Buhari, kuma duk da cewa yanzu haka akwai tsofaffin gwamnoni biyu da ke tsare a gidajen yari bisa zargin almundahana, za a iya cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin har yau ba a dauki matakin magance matsalar tun daga tushe ba.

Har yanzu fa akwai manyan mutanen da ake yi wa zargin cin hanci, amma su na nan su na ta wandaka, hasali ma, irin su aka fi zaba domin wakiltar mutane a majalisun dokoki na kasar nan.

Tunda ya ke shugaban Kasa ya bayyana matsayar shi dangane da matsalar cin hanci da rashawa, yanzu kuma lokaci ya yi, da ya kamata ya karkato hankalin sa a kan matsalar da ta fi addabar al’ummar kasar nan, kamar yadda ya yi alkawarin kawo Canji.

Gaskiyar Magana ita ce, duk yawan mutanen da za a ce shugaban kasa ya daure a kan cin hanci da rashawa, ba zai burge mutane kamar kokarin kare rayukan al’umma, da kuma magance matsanancin talaucin da su ke fama da shi ba.

Cin hanci da rashawa dai ba sa kisa, amma tabarbarewar tsaro da matsanancin talauci su na yi, don haka shugaba Buhari ba ya da wani zabin da wuce daukar matakin kare rayukan al’ummar sa, ta hanyar samar da ingantaccen tsaro, kasancewar mafi yawa daga cikin matsalolin da jama’a ke fuskanta, tabarbarewar tsaro ne musabbabin samuwar su.

Mahimmancin samar da tsaro shi ne kare rayukan al’umma, ta yadda kowa zai iya gudanar da harkokin gaban shi, ba tare da wata fargaba ba, kuma ta haka ne kowa zai iya samun sararin bada gudunmuwar ciyar da kasa gaba.

Mun zabi shugaba Buhari a shekara ta 2015, mun kuma sake zaben shi karo na biyu a shekara ta 2019, saboda yarda da cewa zai iya tsamo Nijeriya da mutanen ta daga mawuyancin halin da su ka tsinci kawunan su, musamman ta yadda kowa zai amfana da albarkatun kasa, idan har an samu nasarar kakkabe cutar cin hanci da rashawa a fadin Nijeriya.

A makon da ya gaba, uwar gidan shugaban kasa A’isha Buhari ta bara, inda aka Ambato ta na cewa ‘A Gaggauta Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci Kafin A Kai Ga Kashe Kowa”.

Jaridar Daily Trust ta ranar 2 ga watan Yuni ta ruwaito A’isha Buhari na cewa, ‘Abin takaici ne, a ce mutanen da su ka zabi shugaba Muhammadu Buhari da zuciya daya, amma a ce an bar ‘yan ta’adda su na yi masu kisan gilla.” Shugaba Buhari ba zai rasa jin wannan ba, kuma in ba irin ta ba, babu wanda zai iya fayyace gaskiyar hakan.

Don haka idan har shugaba Buhari bai saurari furucin uwar gidan shi da idon basira tare da daukar matakin da ya dace ba, to lallai kasar mu na cikin mawuyacin hali.  

Manoman mu na karkara, musamman a jihohin Zamfara da Katsina da Borno duk sun watsar da harkar noma, kawai domin kauce wa kisan gillar ‘yan ta’adda babu gaira babu dalili, ko kuma fadawa tarkon masu garkuwa da mutane.

Haka abin ya ke a sauran jihohin da su ka hada da Benue da Filato, da Kaduna da kuma Taraba.

Idan babu noma babu maganar abinci, idan kuma babu abinci, za a fuskanci matsanancin fari kenan, don haka ya zama wajibi mu koma a kan manyan matsalolin da za su iya salwantar da rayuwar mu domin magance su.

Sannan kada a manta, tabarbarewar tsaro na kara ruruta wutar matsalar cin hanci da rashawa a kasa. Cin hanci ya na ta’azzara ne, matukar aka yi watsi da mutane, wato kowa ya yi sallah da karatun kan sa.

Don haka ta rage ruwan shugaban kasa, ko dai ya cigaba da yaki da cin hanci da rashawa, ko kuma ya fuskanci matsalar tabarbarewar tsaro da ke salwantar da rayuka da dukiyoyin al’ummar sa.

 ‘Yan ta’adda, sun maida rayukan mutane tamkar madafun gudanar da harkokin rayuwar su ta yau da kullum. Gaskiya ba za ta sabu ba ya kai mai girma shugaban kasa, domin tsaro ya fi komai mahimmanci ga al’ummomin Nijeriya, kuma na za san shugaban kasa zai iya yin bakin kokarin sa.

Exit mobile version