Home Labaru Tsoffin Kansiloli 360 Sun Yi Al’Kunuti Kan Hakkinsu A Hannun Gwamnatin Kano

Tsoffin Kansiloli 360 Sun Yi Al’Kunuti Kan Hakkinsu A Hannun Gwamnatin Kano

92
0

Rahotanni daga jihar Kano na cewa, tsofaffin kansiloli sama da 360 ne su ka gudanar da taron addu’ar rokon Allah Ya kai masu dauki game da hakokkin su da Gwamnatin Jihar Kano ta ki biyan su.

Tsofaffin kansilolin sun ce, yawancin su sun hadiye zuciya sun mutu saboda kuncin rayuwa, don haka su ka roki gwamnatin jihar Kano ta dubi halin da su ke ciki.

Yayin su ke zantawa da manema labarai, daya daga cikin su ya ce, sun a son Gwamnatin jihar Kano ta tausaya ta biya su hakokkin su, wanda idan an biya za su samu saukin rayuwa.

Sai dai Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano, ya ce suna sane da hakokkin da tsoffin kansilolin ke bi, amma ya ce yawancin su tun lokacin gwamnatocin da su ka shude su ke bin bashin.

Ya ce gwamnan jihar Kano ba ya da muradin tafiya ya bar gwamnati mai zuwa da tarin bashi kamar yadda ya gada a wajen gwamnatocin baya.

Leave a Reply