Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsofaffin Gwamnoni 10 Da Ke Karbar Kudin Fansho Duk Da Su Na Majalisar Dattawa

Rahotanni na nuni da cewa, yanzu haka akwai akalla sanatoci 13 da har yanzu su ke karbar fansho daga jihohin su a matsayin tsofaffin gwamnoni.

Wannan dai ya na kunshe ne a cikin wani rahoto da gidan talabijin na Arise ya fitar, wanda ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ya nemi a dakatar da fanshon shi na gwamna tunda yanzu ya na matsayin sanata a Majalisar Dattawa.

Gbenga Daniel  dai ya aika da rokon ne a cikin wata takarda da ya rubuta, inda ya bukaci a dakatar da kudin fanshon sa na Naira Dubu dari shida da saba’in da shida, da dari uku da saba’in da shida da Kobo casa’in da biyar na wata-wata da ake ba shi.

Sanatocin da har yanzu dais u ke karbar kudin fansho a matsayin tsofaffin gwamnoni da kuma albashinsu na Majalisar Dattawa sun hada da Godswill Akpabio, da Aliyu Magatakarda Wamakko, da Abdulaziz Yari da Dave Umahi da Aminu Waziri Tambuwal.

Sauran sun hada da Adams Oshiomhole da Ibrahim Hassan Dankwambo da Abubakar Sani Bello da Orji Kalu da Seriake Dickson da Ibrahim Gaidam da Adamu Aliero da kuma Danjuma Goje.

Exit mobile version