Shugaban majalisar Sarakunan jihar Zamfara, Attahiru Ahmad, ya ce jami’an tsaron da a ka jibge a jihar ba su da amfani.
Sarkin ya bayyana haka ne a taron ziyarar da Babban Sufeta janar na ’yan sandan Najeriya Muhammad Adamu, ya kai jihar ta Zamfara, don ganin an shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro a jihar.
Sarkin Zamfaran Anka, ya gargadi shugabannin jami’an tsaro a kan cewa, wannan taron shi ne karo na bakwai, kuma babu wani abinda ya canza, don haka daga yanzu goron gayyatar murnar magance matsalar tsaro ce za su amsa, amma ba na wani taro na daban ba.
Sarkin ya kuma bayyana wa sufeto janar cewa, duk fadin jihar Zamfara ba bu ’yan sanda dubu uku, kuma babu karamar hukumar da ke da ’yan sanda dari da hamsin, sai yace ta yaya za su kare mutum Miliyan hudu dake Zamfara.
Ya nuna rashin gamusuwar su da yadda jami’an tsaro ke nuna halin ko’in-kula a kan kashe rayukan al’ummar jihar Zamfara da kuma garkuwa da su.
Shi kuwa a nasa jawabin Sufeto Janar Muhammad Adamu, ya bayyana jin dadin sa a kan yadda a ka fito ma sa da wasu abubuwan da su ka shige ma sa cikin duhu.
You must log in to post a comment.