Rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Kano, ta sanar da kama wadanda ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban har mutane 90 a makon da ya gabata.
Sabon Kwamishinan ‘yan Sanda na Jihar Ahmed Iliyasu ya bayyana wa manema labarai haka a Hedikwatar Rundunar da ke Bompai birnin Kano.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a farmakin da jami’an tsaro su ka kai wurare da dama da aka yi zargin maboyar batagari ce.
Daga cikin wurare da garuruwan da aka kai farmakin kuwa akwai Gano a Karamar Hukumar Dawakin Kudu, Bachirawa a Karamar Hukumar Ungogo da kuma kan Titin Gidan Sarkin Kano a cikin Karamar Hukumar Birni da Kewaye.
An kuma kama wasu a Dala, da Panshekara, da Kwana Hudu da kuma Dakata duk a cikin Kano.
Daga cikin kayan lahanta jama’a da aka samu a jikin masu laifin akwai wukake 64, da almakasai da dama, da gatari, da awartakin datse karfe, da layu da guraye, da kullin tabar wiwi da kuma madarar sukudaye.