Home Labaru Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane 5 A Wani Hari Da...

Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane 5 A Wani Hari Da Su Ka Kai Jihar Benue

410
0

Akalla mutane biyar su ka mutu, sakamakon wani sabon hari da wasu gungun ‘yan bindiga su ka kai a kauyen Mondo da ke cikin garin Ukembragya-Gaambetiev na karamar hukumar Logo a jahar Benue.

‘yan bindigar, sun banka wasu kauyukan da ke makwaftaka da kauyen Mondo a kan iyakokin jihohin Benue da Taraba da Nasarawa wuta.

Wani shugaba a karamar hukumar Logo Joseph Anawah, ya ce sun samu labarin wasu gungun mahara da su ke kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun fara haurowa yankin su ta cikin ruwa, kwatsam sai ga shi ‘yan bindigar sun kai hari a kauyen Mondo su ka kashe mutane biyar.

Mutanen da aka kashe kuwa sun hada da Torkaa Gbim, da Celina Tavershima, da Ayilaga Tavershima, da Sonter Tavershima da Terkaa Tavershima, sannan akwai wasu da har yanzu babu wanda ya san halin da su ke ciki ko inda su ke.

Shugaban karamar hukumar Logo Richard Nyajo ya shaida wa manema labarai cewa, tabbas ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Mondo, kuma sun kashe mutane biyar tare da jikkata wasu mutane biyu.

Leave a Reply