Home Labarai tsaro: sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗan fashin daji A katsina

tsaro: sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗan fashin daji A katsina

158
0

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka gawurtaccen ɗan-fashin
dajin da ake kira, Maikusa, wanda shi ne mataimakin shugaban
gungun ƴan’ta’adda da suka yi ƙaurin suna wajen addabar
mutane a jihar katsina.


Wanda ke shugabantar gungun ƴanfashin da maikusa ke ciki, an fi kiransa da Modi-Modi.


Dakarun sun ce sun harbe Maikusa da wasu ƴan’ta’adda uku a wata musayar wutar da aka yi a ranar Litinin, 4 ga watan Maris,
2024.

Sojin sun ce an yi arangamar ce a yayin da suke ayyukansu na kawo ƙarshen tayar da ƙayar baya a ƙananan hukumomin Kurfi
da Safana da ke jihar Katsina.


A cewar sojin sun kuma samu nasarar ƙwato bindigogi biyu ƙirar AK-47, da kwanson albarusai 65 da wata bindiga ƙirar
hannu da kakin soji.


Inda suka ƙara da cewa sun kuma lalata maɓoyar ƴan fashin a ƙauyukan Wurma, Shaiskawa, Yauni da Dogon Marke duka a ƙaramar hukumar Kurfi da kuma ƙauyukan Ummadau da Zakka a cikin Safana.

Leave a Reply