Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce dakarun ta sun kashe a kalla ‘yan bindiga biyar bayan sun dakile wani hari da su ka yi yunkurin kai wa a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
Darektan yada labarai da hulda da jama’a na rundunar Ibikunle Daramola ya bayyana haka a ranar litinin din da ta gabata, inda ya ce wasu daga cikin ‘yan bindigar sun tsere da munanan raunukan harbin bindiga a jikin su.
Ya kara da cewa, dakarun soji sun yi nasarar kubutar da wani karamin yaro da wasu mata biyu da ‘yan bindigar su ka yi garkuwa da su.
Daramola ya cigaba da cewa, jami’an sun yi nasarar dakile harin da ‘yan bindigar ne a ranar 31 ga watan Maris, bayan sun samu wasu bayanan sirri da su ka tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga daga dajin Sububu da Kagara na shirin kai hare-hare tare da sace mutane domin yin garkuwa da su.
Ya ce daga nan ne dakarun su suka fara maida martani a kan cikin gaggawa, lamarin ya yi sanadiyar yin musayar wuta a tsakanin ‘yan bindigar.
A karshe ya ce sun samu damar kwace bindigogi kirar Ak-47 guda uku, sannan sun kubutar da wasu mata biyu da wani karamin yaro su ka sace daga wasu kauyukan domin yin garkuwa da su.