Kamfanin kere-kere na hukumar sojin Najeriya ta kera kananan motocin yaki da ayyukan ta’addancin a Najeriya.
Shugaban sojojin kasa, na Najeriya Janar Yusuf Tukur Burutai ne ya bayyana haka a lokacin da yake duba yadda kamfanin ke kera kayan yaki a farfajiyar kamfanin dake Rigachikun a karamar hukumar Igabi jihar Kaduna
Burutai, ya ce kamfanin zai fara kera motocin masu yawa domin ganin an magance matsalolin tsaro da ake fama da su a Najeriya, inda ya bayyana cewa za a nuna kashin farko na kananan motocin da kayan yakin da kamfanin ya hada a ranar 6 ga watan Yuli na wannan shekarar. Burutai ya cewa tun a shekara ta 1960, babu wata hubbasa wajen ganin cewa an rinka hada kayan yaki a cikin Najeriya, amma wannan wani babban ci gaba ne, kuma suna cikin lokaci.
You must log in to post a comment.