Home Labaru Tsaro: Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Ya Bayyana A Gaban Majalisar Dattawa

Tsaro: Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Ya Bayyana A Gaban Majalisar Dattawa

276
0
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Mukaddashin shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu ya bayyana a zauren majalisar dattawa, inda ya yi jawabi a kan halin da tsaron Nijeriya ke ciki.

Wata majiya ta ce Adamu ya fara ziyartar ofishin babban mai ba shugaban kasa shawara a harkokin majalisar dattawa Ita Enang.

Tun farko dai ‘yan majalisar sun gayyaci shugaban ‘yan sandan ne sakamakon halin da tsaron Nijeriya ke ciki, kuma wannan shi ne karo na farko da shugaban ‘yan sandan ya gurfana a gaban majalisar dattawa tun a shekara ta 2014.