Home Labaru Tsaro: Rundunar Sojin Sama Ta Ce Babu Jirgin Da Boko Haram Su...

Tsaro: Rundunar Sojin Sama Ta Ce Babu Jirgin Da Boko Haram Su Ka Harbo A Maiduguri

203
0

Rundunar sojin saman Nijeriya, ta karyata labarun da ke cewa Boko Haram sun harbo wani jirgin yaki a garin Banki da ke jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jirgin majalisar Dinkin Duniya ne ya yi shawagi a sararin saman garin Banki lokacin da ya je yin wani aikin musamman.

Sanarwar ta kara da cewa, jirgin ya koma garin Maiduguri lafiya ba tare da ya samu wata tangarda ba a lokacin aikin.

Kungiyar bada agaji ta majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa, lallai jirgin su ya tafi garin Banki, amma ya koma garin Maiduguri lafiya.