Rundunar sojin kasa ta ce dakarunta sun yi nasarar halaka ‘yan fashi aƙalla 82 a jihohin Katsina da Zamfara
Rundunar musamman ta Operation Hadarin Daji ce ta kai hare-hare ta sama a Birnin Kogo da ke Katsina da kuma Dajin Ajjah na Jihar Zamfara.
Birgediya Janar John Enenche shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba, yana mai cewa ‘yan fashin na ɗauke da manyan makamai ciki har da makamin harbo jirgin sama.
Ya ce an kashe 67 a Birnin Kogo sannan aka halaka 15 a Dajin Ajjah kuma nasarar ta samu ne sakamakon bayanan sirri da suka samu.